Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 9:11-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ubangiji ya ce,“Ke kuma, saboda jinin alkawarina da yake tsakanina da ke,Zan 'yantar da waɗanda suke cikin rami,Waɗanda aka kama daga cikinki.

12. Ku koma mafakarku, ku ɗaurarru masu sa zuciya.Gama yanzu zan sāka muku har ninki biyu.

13. Gama na tankwasa Yahuza ta zama bakana,Na kuma mai da Ifraimu ta zama kibiya,Zan yi amfani da mutanen Sihiyona kamar takobi,Su yi yaƙi da mutanen Hellas.”

14. Ubangiji kuwa zai bayyana kansa gare su,Kibiyarsa za ta fita kamar walƙiya,Ubangiji Allah zai busa ƙaho,Zai taho ta cikin guguwa daga kudu.

15. Ubangiji Mai Runduna zai tsare su,Za su tattake duwatsun majajjawa,Za su sha jini kamar ruwan inabi,Za su cika kamar tasar ruwan inabi,Kamar kuma kusurwoyin bagade.

16. A wannan rana Ubangiji Allahnsu zai cece su,Gama su jama'arsa ne, garkensa kuma,Kamar yadda lu'ulu'u yake haske a kambi,Haka za su yi haske a ƙasarsa.

17. Wane irin kyau da bansha'awa alherinsa yake!Hatsi zai sa samari su yi murna.Sabon ruwan inabi kuma zai sa 'yan mata su yi farin ciki.

Karanta cikakken babi Zak 9