Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 8:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, zan ceci mutanena daga ƙasar gabas da ƙasar yamma.

8. Zan kawo su su zauna a Urushalima. Za su zama jama'ata, ni kuma zan zama Allahnsu da gaskiya da adalci.

9. “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, ku himmantu, ku da kuke jin magana ta bakin annabawa a waɗannan kwanaki tun lokacin da aka ɗora harsashin ginin Haikalin Ubangiji Mai Runduna, don a gina Haikalin.

10. Gama kafin waɗannan kwanaki, mutum da dabba ba su da abin yi. Ba kuma zaman lafiya ga mai fita da shiga saboda maƙiya, gama na sa kowane mutum ya ƙi ɗan'uwansa.

11. Amma yanzu ba zan yi da sauran jama'an nan kamar yadda na yi a kwanakin dā ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.

12. Gama za a yi shuka da salama. Kurangar inabi za ta yi 'ya'ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani, za a yi isasshen ruwan sama. Ni kuwa zan sa sauran jama'an nan su ci moriyar abubuwan nan duka.

13. Ya jama'ar Yahuza da jama'ar Isra'ila, kamar yadda kuka zama abin la'antarwa a cikin al'ummai, haka kuma zan cece ku, ku zama masu albarka, kada ku ji tsoro, amma ku himmantu.

14. “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, kamar yadda na ƙudura in aukar muku da masifa, ban kuwa fasa ba, lokacin da kakanninku suka tsokane ni, suka sa na yi fushi.

15. Haka kuma na ƙudura a waɗannan kwanaki in yi wa Urushalima da jama'ar Yahuza alheri. Kada ku ji tsoro!

16. Abubuwan da za ku yi ke nan, ku faɗa wa juna gaskiya, ku yi shari'a ta gaskiya a majalisunku, domin zaman lafiya.

17. Kada ku ƙulla wa junanku sharri, kada kuma ku so yin rantsuwa ta ƙarya, gama ina ƙin waɗannan abubuwa duka, ni Ubangiji na faɗa.”

Karanta cikakken babi Zak 8