Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 8:12-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Gama za a yi shuka da salama. Kurangar inabi za ta yi 'ya'ya, ƙasa kuma za ta ba da amfani, za a yi isasshen ruwan sama. Ni kuwa zan sa sauran jama'an nan su ci moriyar abubuwan nan duka.

13. Ya jama'ar Yahuza da jama'ar Isra'ila, kamar yadda kuka zama abin la'antarwa a cikin al'ummai, haka kuma zan cece ku, ku zama masu albarka, kada ku ji tsoro, amma ku himmantu.

14. “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, kamar yadda na ƙudura in aukar muku da masifa, ban kuwa fasa ba, lokacin da kakanninku suka tsokane ni, suka sa na yi fushi.

15. Haka kuma na ƙudura a waɗannan kwanaki in yi wa Urushalima da jama'ar Yahuza alheri. Kada ku ji tsoro!

16. Abubuwan da za ku yi ke nan, ku faɗa wa juna gaskiya, ku yi shari'a ta gaskiya a majalisunku, domin zaman lafiya.

17. Kada ku ƙulla wa junanku sharri, kada kuma ku so yin rantsuwa ta ƙarya, gama ina ƙin waɗannan abubuwa duka, ni Ubangiji na faɗa.”

18. Ubangiji Mai Runduna ya yi magana da ni, ya ce,

19. “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, azumi na watan huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai, da na watan goma, za su zama lokatan murna, da farin ciki, da idodin farin ciki, ga jama'ar Yahuza, saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.

20. “Mutanen birane da yawa za su hallara.

Karanta cikakken babi Zak 8