Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Wahayin Karusai Huɗu

1. Na kuma ɗaga idona, sai na ga karusa huɗu suna fitowa daga tsakanin duwatsu biyu. Duwatsun kuwa na tagulla ne.

2. Dawakai aharasai ne suke jan karusa ta fari, ta biyu kuwa akawalai ne suke janta.

3. Na uku kuma dawakai kiliyai ne suke janta, ta huɗu kuwa hurdu ne yake janta.

4. Sa'an nan na ce wa mala'ikan da yake magana da ni, “Mene ne waɗannan, ya ubangijina?”

5. Ya ce mini, “Waɗannan su ne ruhohi huɗu waɗanda suka fito daga sama bayan da sun nuna kansu a gaban Ubangijin duniya duka.

6. Karusar da akawalai suke ja, za ta tafi ƙasar arewa, wadda kuma dawakai kiliyai suke ja, za ta bi su. Wadda kuwa hurde suke ja, za ta tafi ƙasar kudu.”

7. Sa'ad da ingarmun suka fita, sai suka ƙagauta su zagaya duniya don su bincike ta. Ya ce musu kuwa, “Ku tafi, ku bincike duniya, kuna kai da kawowa.” Har kuwa suka yi.

8. Ya kuma kira ni, ya ce, “Duba, waɗanda suka tafi ƙasar arewa sun sa fushin Ubangiji ya huce.”

Kwatancin Naɗawar Yoshuwa

9. Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,

10. “Ka karɓi sadaka daga Heldai, da Tobiya, da Yedaiya waɗanda suka komo daga bautar talala a Babila. A ranar kuma ka tafi gidan Yosiya ɗan Zafaniya.

11. Ka karɓi azurfa da zinariya a wurinsu, ka ƙera kambi, ka sa shi a kan Yoshuwa, ɗan Yehozadak, babban firist.

12. Ka kuwa ce masa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, mutumin da sunansa Reshe, zai yi girma a inda yake, zai kuma gina Haikalin Ubangiji.

13. Shi ne zai gina Haikalin Ubangiji, ya kuma sami girma, ya yi mulki kamar sarki, ya kuma zama firist. Kome kuwa zai tafi daidai.’

14. Kambin zai kasance a Haikalin Ubangiji don tunawa da Heldai, da Tobiya, da Yedaiya, da Yosiya ɗan Zafaniya.

15. “Waɗanda yake nesa za su zo su gina Haikalin Ubangiji. Za ku kuwa sani Ubangiji Mai Runduna ya aiko ni wurinku. Wannan zai faru idan kun yi biyayya sosai da muryar Ubangiji Allahnku.”