Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 4:9-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. “Zarubabel ne ya ɗora harsashin ginin Haikalin nan da hannunsa, shi ne kuma zai gama ginin da hannunsa. Sa'an nan za ka sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni zuwa gare ka.

10. Gama wane ne ya taɓa raina ranar ƙananan abubuwa? Amma za su yi murna da ganin igiyar awo a hannun Zarubabel. Waɗannan fitilu bakwai su ne alama Ubangiji yana kai da kawowa a duniya.”

11. Na ce masa, “Mece ce ma'anar waɗannan itatuwan zaitun da suke wajen dama da hagun alkukin?”

12. Na kuma sāke tambayarsa na ce, “Mece ce ma'anar waɗannan rassan itatuwan zaitun, waɗanda suke kusa da bututu biyu na zinariya, inda mai yake fitowa?”

13. Sai ya ce mini, “Ba ka san ma'anar waɗannan ba?”Na ce, “A'a, ubangijina.”

14. Sa'an nan ya ce, “Waɗannan su ne keɓaɓɓu biyu waɗanda yake tsaye kusa da Ubangijin dukan duniya.”

Karanta cikakken babi Zak 4