Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 4:3-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Akwai itatuwan zaitun biyu kusa da alkukin, ɗaya a wajen dama da kwano, ɗaya kuma a wajen hagun.”

4. Sai ni kuma na ce wa mala'ikan da yake magana da ni, “Mene ne waɗannan, ya ubangijina?”

5. Sa'an nan mala'ikan da yake magana da ni ya ce, “Ba ka san abubuwan nan ba?”Na ce, “A'a, ubangijina.”

6. Sa'an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna.

Karanta cikakken babi Zak 4