Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 4:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Mala'ikan da yake Magana da ni ya komo ya farkar da ni kamar yadda akan farkar da mutum daga barci.

2. Sa'an nan ya ce mini, “Me ka gani?”Sai na ce, “Na ga alkuki wanda aka yi da zinariya tsantsa, da kwano a kansa, da fitilu bakwai a kansa, da butoci bakwai a kan kowace fitilar da yake bisa alkukin.

3. Akwai itatuwan zaitun biyu kusa da alkukin, ɗaya a wajen dama da kwano, ɗaya kuma a wajen hagun.”

4. Sai ni kuma na ce wa mala'ikan da yake magana da ni, “Mene ne waɗannan, ya ubangijina?”

5. Sa'an nan mala'ikan da yake magana da ni ya ce, “Ba ka san abubuwan nan ba?”Na ce, “A'a, ubangijina.”

Karanta cikakken babi Zak 4