Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 2:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da na ɗaga idona, sai ga wani mutum yana riƙe da igiyar awo.

2. Sai na ce, “Ina za ka?”Ya ce mini, “Zan tafi in auna Urushalima don in san fāɗinta da tsawonta.”

3. Sai ga mala'ikan da yake magana da ni, ya fita, sai wani mala'ika kuma ya zo ya sadu da shi.

4. Ya ce masa, “Ka yi gudu, ka faɗa wa saurayin can, cewa za a zauna a Urushalima kamar a ƙauyuka marasa garu, saboda yawan mutane da dabbobi da suke cikinta.

5. Gama zan zama mata garu na wuta kewaye da ita, zan zama daraja a tsakiyarta, in ji Ubangiji.”

6. Ubangiji ya ce, “Yanzu ku gudu daga ƙasar arewa, gama na warwatsa ku a waje kamar iska ta kusurwoyi huɗu na duniya!

7. Ya ke Sihiyona, ku tsere, ku waɗanda kuke zaune a Babila.”

8. Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Bayan ɗaukaka ya aike ni zuwa wurin al'umman duniyan nan da suka washe ku, gama wanda ya taɓe ku, ya taɓi ƙwayar idona.

Karanta cikakken babi Zak 2