Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 14:10-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ƙasa dukka za ta zama fili, daga Geba zuwa Rimmon a kudancin Urushalima. Amma Urushalima za ta kasance a kan tudu, za ta miƙe daga Ƙofar Biliyaminu, zuwa wurin da ƙofa ta fari take a dā, har zuwa Ƙofar Kusurwa, sa'an nan ta miƙe daga Hasumiyar Hananel zuwa wuraren matsewar ruwan inabin sarki.

11. Za a zauna cikin Urushalima lami lafiya, ba sauran la'ana.

12. Ga annobar da Ubangiji zai bugi dukan al'ummai da ita, wato su da suka tafi su yi yaƙi da Urushalima. Naman jikunansu zai ruɓe lokacin da suke a tsaye. Idanunsu kuma za su ruɓe cikin kwarminsu. Harsunansu za su ruɓe a bakunansu.

13. A wannan rana babbar gigicewa daga wurin Ubangiji za ta faɗo musu, har kowa zai kama hannun ɗan'uwansa, ya kai masa dūka.

14. Mutanen Yahuza za su yi yaƙi don su kāre Urushalima. Za a kuma tattara dukan dukiyar al'umman da suke kewaye, su zinariya, da azurfa, da riguna tuli.

15. Annoba irin wannan kuma za ta faɗo wa dawakai da alfadarai, da raƙuma, da jakuna, da dukan dabbobin da suke cikin sansaninsu.

16. Sa'an nan wanda ya ragu daga cikin dukan al'umman da suka kai wa Urushalima yaƙi zai riƙa haurawa zuwa Urushalima kowace shekara, domin yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarkin sujada a lokacin kiyaye Idin Bukkoki.

17. Idan kuwa wata al'umma a duniya ba ta haura zuwa Urushalima domin ta yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarki sujada ba, ba za a yi mata ruwan sama ba.

18. Idan al'ummar Masar ba ta halarci Idin Bukkoki ba, ba za a yi mata ruwan sama ba. Ubangiji kuma zai kawo mata irin annobar da ya kawo wa al'umman da suka ƙi halartar Idin Bukkoki.

19. Wannan shi ne hukuncin da za a yi wa Masar da dukan al'umman da suka ƙi halartar Idin Bukkoki.

20. A wannan rana za a zāna waɗannan kalmomi, wato “Mai Tsarki ga Ubangiji” a kan ƙararrawar dawakai. Tukwanen da suke Haikalin Ubangiji za su zama kamar kwanonin da suke a gaban bagade.

Karanta cikakken babi Zak 14