Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zak 13:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “A ran nan za a buɗe maɓuɓɓuga don wanke zuriyar Dawuda da mazaunan Urushalima daga zunubi da rashin tsarki.

2. A wannan rana fa, ni Ubangiji Mai Runduna, zan shafe sunayen gumaka daga ƙasar, har da ba za a ƙara tunawa da su ba. Zan kuma kawar da annabawa da mugayen aljannu.

3. Idan har yanzu wani ya ci gaba da yin annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa'an nan mahaifinsa da mahaifiyarsa su soke shi sa'ad da yake annabcin.

4. A wannan rana ce kowane annabi zai ji kunyar wahayinsa sa'ad da ya yi annabcin. Ba zai sa rigar gashi don ya ruɗi jama'a ba.

5. Amma zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne, ni manomi ne, gama ƙasa abar mallakata ce tun ina yaro.’

6. Idan wani ya tambaye shi cewa, ‘Waɗannan raunukan da suke a hannuwanka fa?’ Zai ce, ‘Ai, raunuka ne da aka yi mini a gidan abokaina.’ ”

Karanta cikakken babi Zak 13