Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 99:3-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki,Mai Tsarki ne shi!

4. Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai,Ka kawo adalci cikin Isra'ila,Ka kawo adalci da gaskiya.

5. Ku yabi Ubangiji Allahnmu,Ku yi sujada a gaban kursiyinsa!Mai Tsarki ne shi!

6. Musa da Haruna firistocinsa ne,Sama'ila kuma mai yi masa sujada ne.Suka yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa musu.

7. Ya yi magana da su daga girgije,Suka yi biyayya da dokoki da umarnai da ya ba su.

8. Ya Ubangiji Allahnmu, ka amsa wa jama'arka,Ka nuna musu, kai Allah ne mai yin gafara,Amma kakan hukunta su saboda zunubansu.

9. Ku yabi Ubangiji Allahnmu,Ku yi sujada a bisa dutsensa mai tsarki!Ubangiji Allahnmu Mai Tsarki ne!

Karanta cikakken babi Zab 99