1. Ubangiji Sarki ne,Mutane suna rawar jiki,Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi,Duniya ta girgiza.
2. Ubangiji mai iko ne a Sihiyona,Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al'umma.
3. Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki,Mai Tsarki ne shi!
4. Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai,Ka kawo adalci cikin Isra'ila,Ka kawo adalci da gaskiya.
5. Ku yabi Ubangiji Allahnmu,Ku yi sujada a gaban kursiyinsa!Mai Tsarki ne shi!