Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 99:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji Sarki ne,Mutane suna rawar jiki,Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi,Duniya ta girgiza.

2. Ubangiji mai iko ne a Sihiyona,Shi ne yake mulki a bisa dukan sauran al'umma.

3. Kowa da kowa zai yabi sunansa mai girma, Maɗaukaki,Mai Tsarki ne shi!

4. Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai,Ka kawo adalci cikin Isra'ila,Ka kawo adalci da gaskiya.

Karanta cikakken babi Zab 99