Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 96:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku raira sabuwar waƙa ga Ubangiji!Ku raira waƙa ga Ubangiji, ya duniya duka!

2. Ku raira waƙa ga Ubangiji, ku yabe shi!Kowace rana ku ba da labari mai daɗi cewa,“Ya cece mu!”

3. Ku yi shelar ɗaukakar Ubangiji ga sauran al'umma,Ku yi shelar ayyukansa masu girma ga dukan kabilai.

4. Ubangiji da girma yake, tilas a ɗaukaka shi,Tilas a fi jin tsoronsa fiye da dukan alloli.

5. Allolin dukan al'ummai, gumaka ne kawai,Amma Ubangiji ne ya yi sammai.

Karanta cikakken babi Zab 96