Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 94:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, kai Allah ne wanda yake yin hukunci,Ka bayyana fushinka!

2. Kai ne mai yi wa dukan mutane shari'a,Ka tashi, ka sāka wa masu girmankaiAbin da ya dace da su!

3. Har yaushe mugaye za su yi ta murna?Har yaushe ne, ya Ubangiji?

4. Har yaushe za su yi shakiyanci,Su yi ta ɗaga kai?Har yaushe, ya Ubangiji?

5. Suna ragargaza jama'arka, ya Ubangiji,Suna zaluntar waɗanda suke naka.

6. Suna karkashe gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu,Da kuma baƙin da suke zaune a ƙasarmu.

7. Suna cewa, “Ai, Ubangiji ba ya ganinmu,Allah na Isra'ila ba ya lura da abin da yake faruwa!”

8. Ya jama'ata, ƙaƙa kuka zama dakikai, wawaye haka?Sai yaushe za ku koya?

9. Allah ya yi mana kunnuwa, shi ba zai ji ba?Allah ya yi mana idanu, shi ba zai gani ba?

Karanta cikakken babi Zab 94