Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 92:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. A yi shelar madawwamiyar ƙaunarka kowace safiya,Amincinka kuma kowane maraice,

3. Da abubuwan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya,Da amon garaya mai daɗi.

4. Ya Ubangiji,Ayyukanka masu iko suna sa ni murna,Saboda abin da ka aikataIna raira waƙa domin farin ciki.

5. Ayyukanka da girma suke, ya Ubangiji!Tunaninka da zurfi suke!

6. Ga wani abin da wawa ba zai iya sani ba,Dakiki kuma ba zai iya ganewa ba,

7. Shi ne mai yiwuwa ne mugu ya yi girma kamar tsire-tsire,Masu aikata mugayen ayyuka kuma su arzuta,Duk da haka za a hallaka su ɗungum.

8. Gama kai, ya Ubangiji,Maɗaukaki ne har abada.

9. Mun sani maƙiyanka za su mutu,Dukan mugaye kuwa za a yi nasara da su.

10. Ka sa ni na yi ƙarfi kamar bijimi mai faɗa,Ka sa mini albarka da farin ciki.

11. Na ga fāɗuwar maƙiyana,Na ji kukan mugaye.

Karanta cikakken babi Zab 92