Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 92:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Abu mai kyau ne a yi wa Ubangiji godiya,A raira waƙa don girmansa, Allah mafi ɗaukaka,

2. A yi shelar madawwamiyar ƙaunarka kowace safiya,Amincinka kuma kowane maraice,

3. Da abubuwan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya,Da amon garaya mai daɗi.

4. Ya Ubangiji,Ayyukanka masu iko suna sa ni murna,Saboda abin da ka aikataIna raira waƙa domin farin ciki.

Karanta cikakken babi Zab 92