Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 89:42-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

42. Ka ba maƙiyansa nasara,Ka sa dukansu su yi murna.

43. Ka sa makamansa su zama marasa amfani,Ka bari a ci shi da yaƙi.

44. Ka ƙwace masa sandan sarautarsa,Ka buge gadon sarautarsa ƙasa.

45. Ka sa shi ya tsofe kafin lokacinsa,Ka rufe shi da kunya.

46. Har yaushe za ka ɓoye kanka, ya Ubangiji?Har abada ne?Har yaushe fushinka zai yi ta ci kamar wuta?

47. Ka tuna kwanakin mutum kaɗan ne, ya Ubangiji,Ka tuna yadda ka halicci mutane duka masu mutuwa ne!

48. Wa zai rayu har abada, ba zai mutu ba?Ƙaƙa mutum zai hana kansa shiga kabari?

49. Ya Ubangiji, ina ƙaunarka ta dā?Ina alkawaran nan waɗanda ka yi wa Dawuda?

50. Kada ka manta da yadda aka ci mutuncina, ni da nake bawanka,Da yadda na daure da dukan cin mutuncin da arna suka yi mini.

Karanta cikakken babi Zab 89