Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 89:17-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Kana sa mu ci babbar nasara,Da alherinka kakan sa mu yi rinjaye,

18. Sabili da ka zaɓar mana mai kāre mu,Kai, Mai Tsarki na Isra'ila,Kai ne ka ba mu sarkinmu.

19. Ka faɗa wa amintattun bayinka a wahayin da ka nuna musu tun da daɗewa, ka ce,“Na sa kambin sarauta a kan shahararren soja,Na ba da gadon sarauta ga wanda aka zaɓa daga cikin jama'a.

20. Na zaɓi bawana Dawuda,Na naɗa shi sarkinku.

21. Ƙarfina zai kasance tare da shi,Ikona kuma zai ƙarfafa shi.

22. Abokan gābansa ba za su taɓa cin nasara a kansa ba,Mugaye ba za su kore shi ba.

23. Zan ragargaza magabtansa,In karkashe duk waɗanda suke ƙinsa.

24. Zan ƙaunace shi kullum, in amince da shi,Zan sa ya yi nasara kullayaumin.

25. Zan faɗaɗa mulkinsa tun daga Bahar Rum,Har zuwa Kogin Yufiretis.

26. Zai ce mini, ‘Kai ubana ne da Allahna,Kai ne kake kiyaye ni, kai ne Mai Cetona.’

27. Zan maishe shi ɗan farina,Mafi girma daga cikin dukan sarakuna.

28. Zan riƙa ƙaunarsa har abada,Alkawarin da na yi da shi kuma zai tabbata har abada.

Karanta cikakken babi Zab 89