Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 89:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji zan raira waƙarMadawwamiyar ƙaunarka koyaushe,Zan yi shelar amincinka a dukan lokaci.

2. Na sani ƙaunarka za ta dawwama har abada,Amincinka kuma tabbatacce ne kamar sararin sama.

3. Ka ce, “Na yi alkawari da mutumin da na zaɓa,Na yi wa bawana Dawuda alkawari cewa,

4. ‘Daga zuriyarka kullum za a sami sarki,Zan kiyaye mulkinka har abada.’ ”

5. Talikan da suke Sama suna raira waƙa a kanAbubuwan banmamakin da kake yi,Suna raira waƙa kan amincinka, ya Ubangiji.

6. Ba wani kamarka a Sama, ya Ubangiji,Ba wani daga su cikin talikai da yake daidai da kai.

7. Ana girmama ka a cikin majalisar talikai,Duk waɗanda suke kewaye da kai suna yin tsoronka ƙwarai.

8. Ya Ubangiji Allah, Mai Runduna,Ba wani mai iko kamarka,Kai mai aminci ne a kowane abu.

9. Kai kake mulkin haukan teku,Kakan kwantar da haukan raƙuman ruwa.

10. Ka ragargaza dodon nan Rahab, ka kashe shi,Da ƙarfin ikonka ka cinye maƙiyanka.

11. Duniya taka ce, haka ma samaniya taka ce,Kai ne ka halicci duniya da dukan abin da yake cikinta.

Karanta cikakken babi Zab 89