Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 87:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Allah ya gina birninsa a bisa tsarkakan tuddai,

2. Yana ƙaunar birnin Urushalima fiye da kowane wuri a Isra'ila.

3. Ya birnin Allah, ka kasa kunne,Ga abubuwan banmamaki da ya faɗa a kanka.

4. “Sa'ad da na lasafta sauran al'umma da suke yi mini biyayya,Zan sa Masar da Babila a cikinsu,Zan ce da Filistiya, da Taya, da Habasha,Su ma na Urushalima ne.”

5. A kan Sihiyona kuwa za a ce,“Dukan sauran al'umma nata ne.”Maɗaukaki kuwa zai ƙarfafa ta.

6. Ubangiji zai rubuta lissafin jama'o'i,Ya sa su duka cikin jimilla ta Urushalima.

Karanta cikakken babi Zab 87