Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 82:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Allah yana matsayinsa a taron jama'arsa,Yakan zartar da nufinsa a taron alloli.

2. Tilas ku daina yin rashin gaskiya a shari'a,Ku daina goyon bayan mugaye!

3. Ku kāre hakkin talakawa da na marayu,Ku yi adalci ga matalauta,Da waɗanda ba su da mataimaki.

4. Ku kuɓutar da talakawa da matalauta,Ku cece su daga ikon mugaye!

5. “Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye!Kuna zaune cikin duhu,Ga shi, ba adalci a duniya sam!

6. Na faɗa muku, ku alloli ne,Cewa dukanku 'ya'ya ne na Maɗaukaki.

7. Amma za ku mutu kamar kowane mutum,Ku fāɗi kamar kowane basarauce.”

Karanta cikakken babi Zab 82