Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 78:60-72 Littafi Mai Tsarki (HAU)

60. Ya bar alfarwarsa da take a Shilo,Wato wurin da yake zaune a dā, a tsakiyar mutane.

61. Ya yardar wa abokan gāba su ƙwace akwatin alkawari,Inda aka ga ikonsa da darajarsa,

62. Ya ji fushi da jama'arsa,Ya bar abokan gābansu su karkashe su.

63. Aka karkashe samari a cikin yaƙi,'Yan mata kuma suka rasa ma'aura.

64. Aka karkashe firistoci da takuba,Matansu ba su yi makoki dominsu ba.

65. Daga bisani sai Ubangiji ya tashiKamar wanda ya farka daga barci,Kamar jarumi wanda ya bugu da ruwan inabi.

66. Ya tura abokan gābansa baya,Da mummunar kora mai bankunyaDa ba za su sāke tashi ba.

67. Ubangiji ya rabu da zuriyar Yusufu,Bai kuma zaɓi kabilar Ifraimu ba.

68. A maimakonsu sai ya zaɓi kabilar Yahuza.Ya zaɓi Dutsen Sihiyona, wanda yake ƙauna ƙwarai.

69. A can ya gina Haikalinsa,Kamar wurin zamansa a Sama.Ya kafa shi da ƙarfi kamar duniya,Tabbatacce a kowane lokaci.

70. Ya zaɓi bawansa Dawuda,Ya ɗauko shi daga wurin kiwon tumaki,

71. Ya ɗauko shi daga inda yake lura da 'yan raguna.Ya naɗa shi Sarkin Isra'ila,Ya naɗa shi makiyayin jama'ar Allah.

72. Dawuda kuwa ya lura da su da zuciya ɗaya,Da gwaninta kuma ya bi da su.

Karanta cikakken babi Zab 78