Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 78:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Saboda tsara mai zuwa ta koye su,Su kuma su koya wa 'ya'yansu.

7. Ta haka su ma za su dogara ga Allah,Ba za su manta da abin da ya yi ba,Amma a kullum za su riƙa biyayya da umarnansa.

8. Kada su zama kamar kakanninsu,Jama'ar 'yan tawaye marasa biyayya.Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba,Ba su kuwa yi masa aminci ba.

9. Ifraimawa waɗanda suka yi yaƙi da bakkuna da kibauSuka gudu a ranar yaƙi.

10. Ba su kiyaye alkawarinsu da Allah ba,Sun ƙi biyayya da dokokinsa.

11. Sun manta da abin da ya aikata,Da mu'ujizan nan da ya nuna musu.

12. Kakanninsu na kallo sa'ad da Allah ya aikata wata mu'ujizaA filin Zowan a ƙasar Masar.

13. Ya raba teku, ya ratsa da su ta cikinta,Ya sa ruwa ya tsaya kamar bango.

14. Da rana sai ya bi da su da girgije,Da dare kuwa ya bi da su da hasken wuta.

15. Ya tsaga duwatsu, suka buɗe a hamada,Ya ba su ruwa daga cikin zurfafa.

Karanta cikakken babi Zab 78