Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 78:54-63 Littafi Mai Tsarki (HAU)

54. Ya kawo su tsattsarkar ƙasarsa,Ya kawo su a duwatsun da shi kansa ya ci da yaƙi.

55. Ya kori mazaunan wurin sa'ad da jama'arsa suka dirkako,Ya rarraba ƙasar ga kabilan Isra'ila,A nan ya ba su izini su zauna a wurin, a cikin alfarwansu.

56. Amma sai suka yi wa Allah Mai Iko Dukka tawaye,Suka jarraba shi.Ba su kiyaye dokokinsa ba,

57. Amma suka yi tawaye da rashin aminciKamar kakanninsu,Kamar kiban da aka harba da tanƙwararren baka,Waɗanda ba su da tabbas.

58. Suka sa shi ya yi fushi sabodaMasujadansu na arnanci.Suka sa ya ji kishi saboda gumakansu.

59. Allah ya yi fushi sa'ad da ya ga haka,Don haka ya rabu da jama'arsa ɗungum.

60. Ya bar alfarwarsa da take a Shilo,Wato wurin da yake zaune a dā, a tsakiyar mutane.

61. Ya yardar wa abokan gāba su ƙwace akwatin alkawari,Inda aka ga ikonsa da darajarsa,

62. Ya ji fushi da jama'arsa,Ya bar abokan gābansu su karkashe su.

63. Aka karkashe samari a cikin yaƙi,'Yan mata kuma suka rasa ma'aura.

Karanta cikakken babi Zab 78