Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 78:44-54 Littafi Mai Tsarki (HAU)

44. Ya mai da koguna su zama jini,Masarawa kuwa suka kasa sha daga rafuffukansu.

45. Ya aiko da ƙudaje gare su, suka wahalshe su,Kwaɗi suka lalata filayensu.

46. Ya aiko da gamzari don su ci amfanin gonakinsu,Ya aiko da ɗango su lalata gonakinsu.

47. Ya kashe kurangar inabinsu da ƙanƙara,Ya kuma kashe itatuwan ɓaurensu da jaura.

48. Ya karkashe shanunsu da ƙanƙara,Ya kuma karkashe garkunan tumakinsu da na awakinsu da tsawa.

49. Ya buge su da fushinsa mai zafi, da hasalarsa,Ya sa su damuwa ƙwarai,Da ya aiko da mala'iku masu hallakarwa.

50. Bai kanne fushinsa ba,Bai bar su da rai ba,Amma ya karkashe su da annoba.

51. Ya karkashe 'yan fari mazaNa dukan iyalan da suke Masar.

52. Sa'an nan ya bi da jama'arsaKamar makiyayi, ya fito da su,Ya yi musu jagora cikin hamada.

53. Ya bi da su lafiya, ba su kuwa ji tsoro ba,Amma teku ta cinye abokan gābansu.

54. Ya kawo su tsattsarkar ƙasarsa,Ya kawo su a duwatsun da shi kansa ya ci da yaƙi.

Karanta cikakken babi Zab 78