Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 78:35-53 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Sun tuna, ashe, Allah ne mai kiyaye su,Sun tuna Maɗaukaki shi ne Mai Fansarsu.

36. Amma maganganunsu duka ƙarya ne,Dukan abin da suka faɗa kuwa daɗin baki ne kawai.

37. Ba su yi masa biyayya ba,Ba su yi aminci game da alkawarin da suka yi da shi ba.

38. Amma Allah ya yi wa jama'arsa jinƙai,Ya gafarta zunubansu,Bai hallaka su ba.Sau da yawa yakan kanne fushinsa,Ya dakatar da hasalarsa.

39. Yakan tuna su mutane ne kawai,Kamar iskar da take hurawa ta wuce .

40. Sau da yawa suka tayar masa a hamada.Sau da yawa suka sa shi yin ɓacin rai!

41. Suka yi ta jarraba Allah a kai a kai,Suka kuwa sa Mai Tsarki na Isra'ila yin fushi.

42. Suka manta da ikonsa mai girma.Suka manta da lokacin da ya cece su daga abokan gābansu,

43. Lokacin da ya aikata manyan ayyuka da mu'ujizaiA filin Zowan, ta ƙasar Masar.

44. Ya mai da koguna su zama jini,Masarawa kuwa suka kasa sha daga rafuffukansu.

45. Ya aiko da ƙudaje gare su, suka wahalshe su,Kwaɗi suka lalata filayensu.

46. Ya aiko da gamzari don su ci amfanin gonakinsu,Ya aiko da ɗango su lalata gonakinsu.

47. Ya kashe kurangar inabinsu da ƙanƙara,Ya kuma kashe itatuwan ɓaurensu da jaura.

48. Ya karkashe shanunsu da ƙanƙara,Ya kuma karkashe garkunan tumakinsu da na awakinsu da tsawa.

49. Ya buge su da fushinsa mai zafi, da hasalarsa,Ya sa su damuwa ƙwarai,Da ya aiko da mala'iku masu hallakarwa.

50. Bai kanne fushinsa ba,Bai bar su da rai ba,Amma ya karkashe su da annoba.

51. Ya karkashe 'yan fari mazaNa dukan iyalan da suke Masar.

52. Sa'an nan ya bi da jama'arsaKamar makiyayi, ya fito da su,Ya yi musu jagora cikin hamada.

53. Ya bi da su lafiya, ba su kuwa ji tsoro ba,Amma teku ta cinye abokan gābansu.

Karanta cikakken babi Zab 78