Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 78:25-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ta haka suka ci abincin mala'iku.Allah ya ba su iyakar abin da za su iya ci.

26. Sa'an nan sai ya sa iskar gabas ta hura,Da ikonsa kuma ya sa iskar kudu ta tashi.

27. Ya aika da tsuntsaye bisansu kamar ƙura,Yawansu kamar yashi a gaɓa,

28. Sai suka fāɗo a zango,Kewaye da alfarwai ko'ina.

29. Sai mutane suka ci suka ƙoshi,Allah ya ba su iyakar abin da suke bukata.

30. Amma sa'ad da suke cikin ci,Tun ba su ƙoshi ba,

31. Sai Allah ya yi fushi da su.Ya karkashe ƙarfafan mutane,Da samarin Isra'ila na gaske!

32. Ko da yake ya aikata mu'ujizai da yawa,Duk da haka jama'a suka ci gaba da yin zunubi,Ba su kuwa gaskata shi ba.

33. Ta haka ya ƙare kwanakinsu kamar fitar numfashi,Bala'i ya aukar wa rayukansu farat ɗaya.

Karanta cikakken babi Zab 78