Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 78:12-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Kakanninsu na kallo sa'ad da Allah ya aikata wata mu'ujizaA filin Zowan a ƙasar Masar.

13. Ya raba teku, ya ratsa da su ta cikinta,Ya sa ruwa ya tsaya kamar bango.

14. Da rana sai ya bi da su da girgije,Da dare kuwa ya bi da su da hasken wuta.

15. Ya tsaga duwatsu, suka buɗe a hamada,Ya ba su ruwa daga cikin zurfafa.

16. Ya sa rafi ya fito daga cikin dutse,Ya sa ruwan ya yi gudu kamar a kogi.

17. Amma sun ci gaba da yi wa Allah zunubi,A hamada suka yi wa Maɗaukaki tawaye.

18. Da gangan suka jarraba Allah,Da suka ce ya ba su irin abincin da suke so.

19. Suka yi magana gāba da Allah, suka ce,“Ko Allah yana da iko ya ba mu abinci a hamada?

20. Gaskiya ce, ya bugi dutse,Ruwa kuwa ya fito a yalwace,Amma ko yana da iko ya ba da abinci da nama ga jama'arsa?”

21. Saboda haka Allah ya yi fushi sa'ad da ya ji su,Ya aukar wa jama'arsa da wuta,Fushinsa ya haɓaka a kansu,

22. Saboda ba su amince da shi ba,Ba su kuma gaskata yana da ikon cetonsu ba.

23. Amma ya yi magana da sararin sama,Ya umarci ƙofofinsa su buɗe,

24. Ya ba su tsaba daga sama,Da ya sauko musu da manna, su ci.

25. Ta haka suka ci abincin mala'iku.Allah ya ba su iyakar abin da za su iya ci.

Karanta cikakken babi Zab 78