Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 78:10-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ba su kiyaye alkawarinsu da Allah ba,Sun ƙi biyayya da dokokinsa.

11. Sun manta da abin da ya aikata,Da mu'ujizan nan da ya nuna musu.

12. Kakanninsu na kallo sa'ad da Allah ya aikata wata mu'ujizaA filin Zowan a ƙasar Masar.

13. Ya raba teku, ya ratsa da su ta cikinta,Ya sa ruwa ya tsaya kamar bango.

14. Da rana sai ya bi da su da girgije,Da dare kuwa ya bi da su da hasken wuta.

15. Ya tsaga duwatsu, suka buɗe a hamada,Ya ba su ruwa daga cikin zurfafa.

16. Ya sa rafi ya fito daga cikin dutse,Ya sa ruwan ya yi gudu kamar a kogi.

17. Amma sun ci gaba da yi wa Allah zunubi,A hamada suka yi wa Maɗaukaki tawaye.

18. Da gangan suka jarraba Allah,Da suka ce ya ba su irin abincin da suke so.

19. Suka yi magana gāba da Allah, suka ce,“Ko Allah yana da iko ya ba mu abinci a hamada?

Karanta cikakken babi Zab 78