Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 71:17-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Kai ne ka koya mini, ya Allah, tun lokacin da nake yaro,Har wa yau kuwa ina ba da labarin ayyukanka masu banmamaki.

18. Yanzu da na tsufa, na kuma yi furfura,Kada ka rabu da ni, ya Allah!Ka kasance tare da ni sa'ad da nake shelar ikonka da ƙarfinka ga mutanen dukan zamanai masu zuwa.

19. Adalcinka, ya Allah, ya kai har sammai.Ka aikata manyan ayyuka,Ba waninka!

20. Ka aiko mini da wahala da azaba,Amma za ka mayar mini da ƙarfina,Za ka tashe ni daga kabari.

21. Za ka girmama ni har abada,Za ka sāke ta'azantar da ni.

22. Hakika zan yabe ka da garaya,Zan yabi amincinka, ya Allahna.Da garayata zan yi maka waƙoƙi,Ya Mai Tsarki na Isra'ila.

23. Zan ta da muryar farin cikiSa'ad da nake raira maka waƙar yabbai,Zan raira waƙa da zuciya ɗaya,Gama dā ka fanshe ni.

24. Zan yi magana a kan adalcinka dukan yini,Saboda an yi nasara da waɗanda suke ƙoƙari su cuce ni, sun ruɗe.

Karanta cikakken babi Zab 71