Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 71:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A gare ka, ya Ubangiji, lafiya lau nake,Faufau kada ka bari a yi nasara da ni!

2. Sabili da kai adali ne ka taimake ni, ka cece ni.Ka kasa kunne gare ni, ka cece ni!

3. Ka zama mini lafiyayyiyar mafaka,Da kagara mai ƙarfi, domin ka tsare ni,Kai ne mafakata da kāriyata.

4. Ya Allahna, ka cece ni daga mugaye,Daga ikon mugga, wato mugayen mutane.

5. Ya Ubangiji, a gare ka nake sa zuciya,Tun ina yaro, nake dogara gare ka.

6. A duk kwanakina a gare ka nake dogara,Kana kiyaye ni tun da aka haife ni,Kullayaumi zan yabe ka!

7. Raina abin damuwa ne ga mutane da yawa,Amma kai ne kāriyata mai ƙarfi.

8. Ina yabonka dukan yini,Ina shelar darajarka.

9. Yanzu da na tsufa, kada ka yashe ni,Yanzu da ƙarfina ya ƙare kuma, kada ka rabu da ni!

10. Maƙiyana, waɗanda suke so su kashe ni,Suna magana, suna ƙulle-ƙulle gāba da ni.

11. Suna cewa, “Ai, Allah ya rabu da shi,Gama ba wanda zai cece shi!”

Karanta cikakken babi Zab 71