Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 67:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka yi mana jinƙai, ya Allah, ka sa mana albarka,Ka dube mu da idon rahama,

2. Domin dukan duniya ta san nufinka,Dukan sauran al'umma kuma su san cetonka.

3. Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah,Da ma dukan mutane su yabe ka!

4. Da ma sauran al'umma su yi murna, su raira waƙa ta farin ciki,Domin kana yi wa jama'a shari'a ta adalci,Kana kuma bi da dukan sauran al'umma.

5. Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah,Da ma dukan mutane su yabe ka!

Karanta cikakken babi Zab 67