Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 63:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sa'ad da nake kwance a gadona na tuna da kai,Dare farai ina ta tunawa da kai,

7. Domin kai kake taimakona kullayaumin.Da murna, nake raira waƙa,A inuwar fikafikanka,

8. Raina yana manne maka,Ikonka yana riƙe da ni.

9. Waɗanda suke ƙoƙari su kashe ni,Za su gangara zuwa lahira,

10. Za a kashe su cikin yaƙi,Kyarketai kuwa za su cinye gawawwakinsu.

Karanta cikakken babi Zab 63