Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 60:9-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ya Allah, wa zai kai ni birni mai kagara?Wa zai kai ni Edom?

10. Da gaske ka yashe mu ke nan?Ba za ka yi tafiya tare da sojojinmu ba?

11. Ka taimake mu, mu yaƙi abokan gāba,Domin taimako irin na mutum banza ne!

12. Idan Allah yana wajenmu,Za mu yi nasara,Zai kori abokan gābanmu.

Karanta cikakken babi Zab 60