Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 56:7-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ka hukunta su, ya Allah saboda muguntarsu,Da fushinka ka kori waɗannan mutane!

8. Ka san irin wahalar da nake sha,Kana riƙe da lissafin yawan hawayena.Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba?

9. A ranar da na yi kira gare ka,Za a komar da abokan gābana baya,Gama na sani Allah yana tare da ni!

10. Ina dogara ga Allah, ina yabon alkawarinsa,Ina dogara ga Ubangiji, ina yabon alkawarinsa.

Karanta cikakken babi Zab 56