Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 55:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. In tafi can nesa,In yi wurin zamana a hamada.

8. Zan hanzarta in nemi mafakaDaga iska mai ƙarfi da hadiri.”

9. Ka hallaka su, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu,Gama na ga hargitsi da tawaye a birni.

10. Dare da rana suna ta yawo a kan garu suna ta kewaye birnin,Birnin kuwa cike yake da laifi da wahala.

11. Akwai hallaka a ko'ina,Tituna suna cike da azzalumai da 'yan danfara.

12. Da a ce maƙiyina ne yake mini ba'a,Da sai in jure.Da a ce abokin gābana ne yake shugabancina,Da sai in ɓuya masa.

13. Amma kai ne, aminina,Abokin aikina ne, abokina ne kuma!

14. Dā mukan yi taɗi da juna ƙwarai,Mukan tafi Haikali tare da sauran jama'a.

15. Allah ya sa mutuwa ta auko wa maƙiyana ba labari,Allah ya sa su gangara ƙasar matattu da ransu!Mugunta tana cikin gidajensu da zukatansu.

16. Amma ina kira ga Allah, yă taimake ni,Ubangiji kuwa zai cece ni.

Karanta cikakken babi Zab 55