Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 55:6-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Na ce, “Da a ce ina da fikafikai kamar kurciya,Da sai in tashi, in tafi, in nemi wurin hutawa!

7. In tafi can nesa,In yi wurin zamana a hamada.

8. Zan hanzarta in nemi mafakaDaga iska mai Æ™arfi da hadiri.”

9. Ka hallaka su, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu,Gama na ga hargitsi da tawaye a birni.

10. Dare da rana suna ta yawo a kan garu suna ta kewaye birnin,Birnin kuwa cike yake da laifi da wahala.

Karanta cikakken babi Zab 55