Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 55:15-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Allah ya sa mutuwa ta auko wa maƙiyana ba labari,Allah ya sa su gangara ƙasar matattu da ransu!Mugunta tana cikin gidajensu da zukatansu.

16. Amma ina kira ga Allah, yă taimake ni,Ubangiji kuwa zai cece ni.

17. Koke-kokena da nishe-nishenaSuna hawa zuwa gare shi da safe, da tsakar rana, da dad dare,Zai kuwa ji muryata.

18. Zai fisshe ni lafiyaDaga yaƙe-yaken da nakan yi da magabtana masu yawa.

19. Allah, shi wanda yake mulki tun fil azal,Zai ji ni, zai kore su.Ba abin da suka iya yi a kai,Domin ba su tsoron Allah.

20. Abokina na dā,Ya yi wa abokansa faɗa,Ya ta da alkawarinsa.

21. Kalmominsa sun fi mai taushi,Amma ƙiyayya tana a zuciyarsa,Kalmominsa sun fi mai sulɓi,Amma suna yanka kamar kakkaifan takobi.

22. Ka gabatar da wahalarka ga Ubangiji,Zai kuwa taimake ka,Ba zai bari a ci nasara a kan mutumin kirki ba, faufau.

23. Amma kai, ya Allah, za ka jefar da masu kisankai, da maƙaryata can ƙasa cikin zurfafa,Kafin su kai rabin kwanakinsu a duniya.Amma ni, zan dogara gare ka.

Karanta cikakken babi Zab 55