Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 55:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka ji addu'ata, ya Allah,Kada ka ƙi jin roƙona!

2. Ka saurare ni, ka amsa mini,Gama damuwata ta gajiyar da ni tiƙis.

3. Hankalina ya tashi saboda yawan kurarin maƙiyana,Saboda danniyar mugaye.Sukan jawo mini wahala,Suna jin haushina suna ƙina.

4. Azaba ta cika zuciyata,Tsorace-tsoracen mutuwa sun yi mini nauyi.

5. Tsoro da rawar jiki sun kama ni,Na cika da razana.

6. Na ce, “Da a ce ina da fikafikai kamar kurciya,Da sai in tashi, in tafi, in nemi wurin hutawa!

7. In tafi can nesa,In yi wurin zamana a hamada.

8. Zan hanzarta in nemi mafakaDaga iska mai ƙarfi da hadiri.”

Karanta cikakken babi Zab 55