Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 52:6-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Adalai za su ga wannan, su ji tsoro,Za su yi maka dariya, su ce,

7. “Duba, ga mutumin da bai dogara ga AllahDon ya sami zaman lafiyarsa ba.A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa.Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.”

8. Amma ni, kamar itacen zaitun nake, wanda yake girma kusa da Haikalin Allah,Ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa har abada abadin.

9. Zan gode maka, ya Ubangiji,Saboda abin da ka aikata.Zan dogara gare ka,Sa'ad da nake sujada tare da jama'arka,Domin kai mai alheri ne.

Karanta cikakken babi Zab 52