Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 50:13-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Nakan ci naman bijimai ne?Ko nakan sha jinin awaki?

14. Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya,Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.

15. Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo,Zan cece ku,Ku kuwa za ku yabe ni.”

16. Amma Allah ya ce wa mugaye,“Don me za ku haddace umarnaina?Don me za ku yi magana a kan alkawaraina?

17. Kun ƙi in tsauta muku,Kun yi watsi da umarnaina.

18. Sa'ad da kuka ga ɓarawo kukan yi abuta da shi.Kuna haɗa kai da mazinata.

19. “Kullum a shirye kuke ku hurta mugunta,Ba ku jin nauyin faɗar ƙarya.

20. A shirye kuke ku sari 'yan'uwanku,Ku sa musu laifi.

21. Kun aikata waɗannan duka, ni kuwa ban ce kome ba,Saboda haka kuka zaci ni kamar ku nake.Amma yanzu zan tsauta muku,In bayyana muku al'amarin a fili.

22. “Ku ji wannan ku da kuke ƙyale ni,In ba haka ba zan hallaka ku,Ba wanda zai cece ku.

23. Wanda yake yin godiya a sa'ad da yake miƙa hadayarsa, yana girmama ni,Da wanda yake yi mini biyayya kuma, zan nuna masa cetona.”

Karanta cikakken babi Zab 50