Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 49:10-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Yakan sa masu hikima su ma su mutu,Haka nan ma wawaye da mutanen banza,Za su mutu su bar dukiyarsu ga zuriyarsu.

11. Kaburburansu za su zama gidajensu har abada,Can za su kasance kullum,Ko da yake a dā suna da ƙasa ta kansu.

12. Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba,Zai mutu kamar dabba.

13. Dubi abin da zai faru ga waɗanda suke dogara ga kansu,Da irin ƙaddarar waɗanda dukiya ta ishe su.

14. Za a ƙaddara su ga mutuwa kamar tumaki,Mutuwa ce za ta yi kiwonsu.Da safe adalai za su ci nasara a kansu,Sa'ad da gawawwakinsu suke ruɓewa a ƙasar matattu,Nesa da gidajensu.

15. Amma Allah zai fanshe ni,Zai ɗauke ni daga ikon mutuwa.

16. Kada ka damu sa'ad da mutum ya zama attajiri,Ko kuwa dukiyarsa ta ƙasaita,

17. Domin ba zai ɗauke ta a lokacin mutuwarsa ba,Dukiyarsa ba za ta shiga kabari tare da shi ba.

18. Ko da a ce mutum ya sami falalar wannan rai,Ana kuwa ta yabonsa saboda nasarar da ya ci,

19. Duk da haka zai tarar da kakanninsa waɗanda suka mutu,Inda duhu ya dawwama har abada.

20. Girman mutum ba zai hana shi mutuwa ba,Zai mutu kamar dabba.

Karanta cikakken babi Zab 49