Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 47:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku yi tāfi saboda farin ciki,Ya ku jama'a duka!Ku raira waƙoƙi da karfi, ku yabi Allah!

2. A ji tsoron Ubangiji Mai Iko Dukka,Shi babban Sarki ne, ya mallaki dukan duniya.

3. Ya ba mu nasara a bisa jama'o'i,Ya sa muka yi mulkin al'ummai,

4. Ya zaɓar mana ƙasar da muke zaune,Wadda take mallaka ce ta fāriya, ta jama'arsaWadda yake ƙauna.

5. Allah ya hau kan kursiyinsa!Aka yi ta sowa ta murna, ana ta busa ƙahoni,Lokacin da Ubangiji yake hawa!

6. Ku raira yabbai ga Allah,Ku raira yabbai ga sarkinmu!

7. Allah sarki ne na duniya duka,Ku yabe shi da waƙoƙi!

Karanta cikakken babi Zab 47