Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 46:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.

2. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba,Ko da duniya za ta girgiza,Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku,

3. Ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa,Tuddai kuma su girgiza saboda tangaɗin tekun.

4. Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah,Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki.

5. Allah yana zaune cikin birnin,Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau.Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa.

6. An kaɓantar da sauran al'umma, mulkoki suka girgiza,Allah ya yi tsawa, duniya kuwa ta narke.

7. Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu,Allah na Yakubu shi ne mafakarmu!

8. Zo ku ga abin da Ubangiji ya yi!Dubi irin ayyukan al'ajabi da ya yi a duniya!

Karanta cikakken babi Zab 46