Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 46:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu,Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala.

2. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba,Ko da duniya za ta girgiza,Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku,

3. Ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa,Tuddai kuma su girgiza saboda tangaɗin tekun.

4. Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah,Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki.

5. Allah yana zaune cikin birnin,Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau.Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa.

Karanta cikakken babi Zab 46