Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 43:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Allah, ka kuɓutar da ni,Ka kiyaye al'amarina daga marasa tsoronka,Ka cece ni daga ƙaryar mugaye!

2. Ya Allah, kai ne kake kāre ni,Me ya sa ka yashe ni?Me ya sa nake ta shan wahala saboda muguntar maƙiyana?

3. Ka aiko da haskenka, da gaskiyarka,Bari su bishe ni,Su kawo ni Sihiyona, tsattsarkan tudunka,Su kawo ni Haikalinka, inda zatinka yake!

4. Sa'an nan zan tafi wurin bagadenka, ya Allah,Zuwa gare ka, kai wanda kake sa ni in yi murna da farin ciki,In raira waƙar yabo a gare ka da garayata,Ya Allah, Allahna!

5. Me ya sa nake baƙin ciki?Me ya sa nake damuwa?Zan dogara ga Allah,Zan ƙara yabonsa,Mai Cetona, Allahna.

Karanta cikakken babi Zab 43