Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 40:12-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Wahalai iri iri sun kewaye ni, har ba su ƙidayuwa!Alhakin zunubaina ya tarar da ni,Har ba na iya gani,Sun fi gashin kaina yawa, na karaya.

13. Ka cece ni, ya Allah,Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni!

14. Ka sa masu so su kashe ni,A ci nasara a kansu, su ruɗe!Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalainaSu koma baya, su sha kunya!

Karanta cikakken babi Zab 40