Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 4:2-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Ku mutanen nan, sai yaushe za ku daina zagina?Sai yaushe za ku daina ƙaunar abubuwan banza,Da bin abin da yake na ƙarya?

3. Ku tuna fa, Ubangiji ne ya zaɓe ni domin in zama nasa,Ya kuma ji ni lokacin da na yi kira gare shi.

4. Ku ji tsoro, ku daina aikata zunubinku,Ku yi tunani da gaske a kan wannanA kaɗaice, shiru, a ɗakunanku.

5. Ku miƙa wa Ubangiji hadayun da suka dace,Ku kuma dogara gare shi.

6. Akwai mutane da yawa da suke cewa,“Da ma a sa mana albarka!”Ka dube mu da alheri, ya Ubangiji!

7. Farin cikin da ka ba ni mai yawa ne,Fiye da na waɗanda suke da wadataccen hatsi da ruwan inabi.

8. Da zarar na kwanta, sai barci ya kwashe ni,Kai kaɗai kake kiyaye ni sosai, ya Ubangiji.

Karanta cikakken babi Zab 4