Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Zab 4:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka amsa mini sa'ad da na yi kira,Ya Allah, madogarata!Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona.Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu'ata!

2. Ku mutanen nan, sai yaushe za ku daina zagina?Sai yaushe za ku daina ƙaunar abubuwan banza,Da bin abin da yake na ƙarya?

3. Ku tuna fa, Ubangiji ne ya zaɓe ni domin in zama nasa,Ya kuma ji ni lokacin da na yi kira gare shi.

4. Ku ji tsoro, ku daina aikata zunubinku,Ku yi tunani da gaske a kan wannanA kaɗaice, shiru, a ɗakunanku.

5. Ku miƙa wa Ubangiji hadayun da suka dace,Ku kuma dogara gare shi.

6. Akwai mutane da yawa da suke cewa,“Da ma a sa mana albarka!”Ka dube mu da alheri, ya Ubangiji!

Karanta cikakken babi Zab 4